Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoHar yanzu Ganduje ne gwamna - Gwamnatin Kano | Premier Radio |...

Har yanzu Ganduje ne gwamna – Gwamnatin Kano | Premier Radio | 31.03.2023

Date:

Muhammad Bello Dabai

Gwamnatin Kano ta yi kira ga gwamna mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf na NNPP, da ya tsahirta kan fitar da sanarwa da sunan baiwa jama’a shawara har zuwa lokacin da za a rantsar da shi.

Ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ya fitar, dake a matsayin martani kan kalaman Abba Kabir na baiwa jama’a shawarar kauracewa sayen filayen gwamnati.

Abba Kabir dai ya fitar da sanarwar ce, yana mai jan kunnen masu sayen filayen makarantu, makabarta, asibitai da sauransu, da cewar duk abinda ya biyo baya su suka siya da kudinsu.

To sai dai, sanarwar da gwamnatin Kanon ta fitar, ta bayyan lamarin a matsayin kutse ga manufofin gwamnati mai ci, wanda ka iya haifar da rashin fahimta tsakanin al’umma.

Sanarwar ta kara cewa matukar Abba bai karbi rantsuwar shiga ofishi ba, to ba shi da iko irin na gwamna.

Tace ko da bayan rantsuwa, ba komai zai iya sauyawa da gwamnati ta kawo ba sai tsirari.

Har ila yau, gwamnatin Kanon ta bukaci daidaikun mutane da kamfanonin da suka mallaki filaye ta halastacciyar hanya kan su kwantar da hankulansu.

Tun bayan fitar sanarwar, wadda sakataren yada labaran zababben gwamnan, Sanusi Bature ya fitar, batun ke cigaba da yamutsa hazo a shafukan sada zumunta, inda ake wallafa hotunan filayen da ake zargin gwamnati da siyarwa, ko kuma ginewa ba bisa ka’ida ba.

Latest stories

Related stories

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...