Domin ka sani

Premier Radio 107.7 tashar labarai ce da al’amuran yau-da-kullum, da nishadin iyali, da ke tare da makarantar koyon aikin jarida, kuma duka mallaki ne na kamfanin Media Support Systems Limited.

Wannan gidan Rediyo ya kware a labarai da shirye-shirye, inda milyoyin mutane ke sauraro da`kallonmu a kafofin sadarwa na zamani, wato ‘soshiyal media’.

Premier Radio na watsa shirye-shiryenta a harshen Hausa (95%) da turanci (5%).

Ita kuma makarantar Premier Media Academy ta na bayar da damar samun horo kan dabarun aikin jarida a zamanance, da al’amuran da su ka shafi wasannin kwaikwayo da shirya Fina-finai domin bukatun mutanen Kano da kasa bakidaya.

Manufar mu…

Taimakawa wajen tabbatar da jagoranci nagari, da azzzama jam;a shiga harkokin dimokuradiyya, da sa ido domin tabbatar da adalci da gaskiya a sha’anin shugabancin al’umma.

Burin mu ne mu kasance Rediyon da ta zama jagaba a labarai da shirye-shirye, da wasanni, da nishadin iyali, da al’amuran yau-da-kullum a Nijeriya.

Abun da mu ka sanya gaba shi ne sanar da jama’a halin da jihar Kano ke ciki, da kasa, da duniya bakidaya; mu ilmintar da su, da sanya su cikin nishadi, tare da karfafa musu gwiwa a harkokin zamantakewarsu.

Premier Radio dandalin musayar ra’ayi ce ta hanyar kwarewa, ba tare da son rai ko nuna fifiko ba.

Don haka abubuwan da mu ke son cimma sun hada da:

. Tabbatar da kare al’adun Kanawa ta hanyar kara fito da gargajiyarsu, dabi’unsu da addininsu a tafarkin zamantakewa.

. Samar da kafar labarai mai zaman kan ta da za ta kasance abun dogaro wajen sanin al’amuran yau-da-kullum, da za su gamsar da bukatun jama’a.

. Tabbatar da ganin gidan rediyon Premier ya karfafa yanayi ko salon dimokuradiyyarmu, ta hanyar ba kowa ‘yancin fadin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ba.

Ayyukan da mu ke yi:

. Tallace-tallacen rediyo, da na kafofin intanet, da gyara, ko ingantawa da kyautata rubuce-rubuce a kafofin sadarwar zamani, wato soshiyal media.

. Tace labarai da rubuce-rubucen adabi, da aikin jarida, da koyar da dabarun tafiyar da harkokin kafofin labarai.

. Bayar da`horo kan ayyukan kafofin labaran zamani, da wasannnin kwaikwayo, da aikin rediyo da talbijin, da harkokin shugabanci.

. Mu na hada shirye-shiryen bidiyo, mu kuma tsara maka yadda kayan ka za su yi saukin shiga kasuwa.

. Premier Radio na da budadden dakin wasan kwaikwayo (Open-air Theatre) domin gabatar da wasanni da bukukuwan musamman.

 

Masu sauraronmu:

. Maza da mata daga shekaru goma zuwa hamsin da biyar ko abun da ya zarta haka.

. Ma’aurata, wato mata da miji, da sabon aure- ango da amarya, da wadanda ke shirin daura aure, da ma’aikata ko wadanda ke neman gurbin aiki, ‘yan makaranta da masu bukata ta musamman.

Shugabanni da jagororin al’umma daga kungiyoyi, kwararrun ‘yan kasuwa, da masu fada aji kan al’amuran jama’a daban-daban.

Dukkan wadannan rukunin mutane na zaune a Kano da makwabtan jihohi, da sauran sassan kasar nan da ketare.

 

Ma’aikatan mu:

Mukhtar Yahya Usman-Manajan Labarai da al’amuran yau-da-kullum.

Malam Mukhtar kwararren dan jarida ne,kuma mai fafutukar tabbatar da adalci da ya` shafe shekaru goma yana wannan sana’a. Yana da kyakkyawar hulda da abokan aiki da ma dukkan jama’a.

Ya fara aiki a Freedom Radio a shekarar 2012 inda ya samu gogewa sosai har ya kai matsayin shugaban sashen al’amuran kasashen waje. Ya kuma rike mukamin Editan jaridar ‘Kano Focus da ake wallafawa ta intanet.

Takardun shaidar ilminsa sun hada da Diploma da digiri na biyu, wato Masters, da ya samu a Jami’ar Bayero, da Northwest University Kano. Ya yi rubuce-rubuce da dama da su ka samu martani kan alkiblarsu bisa wasu manufofin kasar nan.

 

Kabiru Garba Haruna Sheka-Manajan sashen siyasa.

Kabiru ya samu shaidar aikin rediyo da daukar hoto daga makarantar koyon aikin jarida ta Gwauron Dutse kafin shiga Jami’ar Bayero inda ya samu babbar Diploma a aikin jarida.

Ya fara aiki a Freedom Radio sannan ya koma Vision Radio Abuja inda ya yi aikin shekara biyar a sassa daban daban, daga nan sai aka nada shi manajan shirye-shirye a Progress Radio Gombe kafin daga baya ya koma Prestige Radio Minna a jihar Neja a dai wannan matsayi na manajan shirye-shirye.

A watan Disambar 2020 sai Kabiru ya`komo gida Kano domin taimakawa wajen kafa wata sabuwar tashar Rediyo inda nan ma ya rike mukamin manajan shirye-shirye.

Ya halarci kwasa-kwasai da dama, ciki har da na BBC Media Action, da PEN University a Lagos, tare da samun horo kan bincike a aikin jarida daga Gidauniyar Mac-Authur da Gidan Rediyon BBC.

Kabiru Sheka na daga cikin ‘yan jaridar farko da suka fara aiki a sabuwar tashar Premier Radio a watan Disambar 2021 inda ya fara da mukamin manajan shirye-shirye.

 

Muhammad Aminu Jolly-Manajan sashen Talla.

Muhammad Aminu tsohon ma’aikacin rediyo ne, kwararren injiniya da harkokin mulki da aikin banki da ya samu shahara a gidan Radio Kano 11 FM lokacin da ya ke gabatar da shirin ‘a Jolly Good Show’ inda sunan Jolly ya makale masa.

Tsawon shekaru fiye da talatin da ya yi yana aiki, Malam Aminu Jolly ya rike mukamin jami’in kade-kade da tsara` shirye-shirye a Cool/Wazobia FM kafin daga baya ya zama manajan shirye-shirye a Guarantee Radio.

 

Nuhu Tahir-Mai kula da harkokin kasuwanci da ayyukan rediyo na kullum.

Shi ma Malam Nuhu tsohon ma’aikacin Rediyo ne,kuma ya fara aiki ne da` kamfanin taba sigari na British American a matsayin jami’in harkokin kasuwanci da ke wakiltar arewacin kasar nan, amma shigarsa aikin rediyo sosai ya fara ne a shekarar 1990 a matsayin manajan tallace-tallace kawo yanzu,inda ya samu damar kulla alaka da cibiyoyin ciniki da harkokin nkasuwanci da dama a kasar nan.

Yan a daga cikin mutanen farko da su ka kafa Nigeria Info a Lagos, wata cibiyar tattara bayanai kan harkokin kasuwanci, kuma shi ne manajan farko na gidan Rediyo da Talbijin na Al-Ansar a Maiduguri, kuma wanda ya zama kwararren jami’in tuntuba kan harkokin talla na gidan Talbijin na Arewa 24.

Kuma da Nuhu Tahir aka kafa gidajen rediyo na Coolwazobia a nan Kano, da Invicta FM a Kaduna.

Shi ne ya jagoranci sake tsarin tashoshin Dala FM da Freedom Radio, kuma har yanzu bai gajiya ba wajen taimakawa da shawarwari ga kafofin labarai a kasar nan.