Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, May 16, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar Hisba ta jihar Kano zata aurar da 'yan jarida 50

Hukumar Hisba ta jihar Kano zata aurar da ‘yan jarida 50

Date:

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da ware wa ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai gurbin mutane 50 a auren gata da za a sake yi a jihar.

Daurawa ya ce shirin na da nufin karfafa alaka a tsakanin ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Sheikh Daurawa ya bayyana nasarar da hukumar ta yi a baya, na aurar da mutane 1,800.

Hakan ne ya sa shugaban na Hisbah ya ce hukumar ta yanke shawarar fadada shirin zuwa fannoni daban-daban kamar aikin jarida, doka, da kiwon lafiya.

Sai dai Daurawa bai sanar da ranar da za a fara shirin kashi na biyu na auren gatan ba.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...