Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET ta yi hasashen samun ambaliyar ruwa a damunar bana a kananan hukumomi 14 cikin 44 na jihar Kano.

Jam’in hukumar da ke kula da Kano da Jigawa Dr Nurudden Abdullahi ne ya sanar da hakan yayın taron masu ruwa da tsaki kan magance haddura masu tasowa da ya gudana a nan Kano.

Dr Nurudden ya bayyana kananan hukumomi da abun zai shafa da suka hadar da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garum Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da kumaDala.

Ya kuma ce wasu kananan hukumomi biyar da suka hadar da Karaye, Takai, Bunkure, Dawakin Tofa da Makoda, za su fuskanci ambaliayar amma matsakaiciya.

Haka kuma ya ce sauran kananan hukumomin 25 da suka hadar da Doguwa, Tudun Wada, Kibiya, Garko, Albasu, Gaya, Kiru, Rogo, Gwarzo, Shanono, Tsanyawa, Bagwai, Bichi, Kunchi, Danbatta, Minjibir, Gabasawa, Gwale, Fagge, Nassarawa, Kano Municipal, Tarauni, Ungogo, Kumbotso and Gezawa zai zo musu da sauki.

 

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...