A halin da ake ciki kuma, rahotanni sun tabbatar da cewa, ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry, ya gana da takwaransa na Faransa dangane da yadda za a tsagaita wuta a Zirin Gaza domin kawo karshen zubar da jinin Falasdinu da Isra’ila ke yi.
Ziyarar da ministan harkokin wajen Faransa Stephane Sejourne ya kai birnin Alkahira, ta zo ne bayan ganawar wakilan Amurka da Masar da Qatar a farkon wannan mako, inda Isra’ila ta gabatrwa kungiyar Hamas tayin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana arba’in.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto mayakan Hamas na nazari kan wannan tayi da ya kunshi musayar fursunoni tsakaninsu da Isra’ila, kusan wata bakwai bayan barkewar yaki a Zirin Gaza.
Shugaban Hamas, Suhail al-Hindi, ya shaidawa manema labarsai cewa, nan ba da jimawa ba zasu bayyana matsayarsu game da wannan batu.
Haka-zalika, Isra’ila ta ce ta na kan tattaunawa, tare da jiran amsar kungiyar Hamas.
 AAG