Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƳan majalisar wakilan Amurka 57 sun tsawatar kan mamayar birnin Rafah.

Ƴan majalisar wakilan Amurka 57 sun tsawatar kan mamayar birnin Rafah.

Date:

Gwamnatin shugaba Joe Biden ta kasar Amurka na shan sabuwar suka daga jam’iyyar Democrat, inda ta ke neman ya hana Isra’ila ƙaddamar da cikakkiyar mamaya a Rafah, birnin da kimanin rabin mutanen Gaza milyan biyu da dubu dari hudu ke samun mafaka.
Rahotanni sun ce, ‘yan majalisar wakilai hamshin da bakwai daga cikin 212 na jam’iyyar sun rattaba hannu kan wata wasiƙa, inda suka yi kira ga gwamnatin Biden ta tsawatawar da Firaiminista Benjamin Netanyahu mai kunnen-ƙashi daga mamayar birnin Rafah, da ke kan iyakar Masar.

A jiya Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce har yanzu bai ga wani shirin Isra’ila na ƙaddamar da mamaya a Rafah ba, yana mai jaddada cewa, mahukunta a Washington ba za su goyi bayan hakan ba.

Tuni dai wasu ɗaliban Jami’ar Fordham a birnin New York suka kafa sansani, inda suke nuna goyon baya ga al’ummar Gaza, a wani mataki na bin sawun takwarorinsu a faɗin Amurka da ke kira a kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa Falasɗinawa.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...