Shugaban Colombia Gustavo Petro ya sanar da yanke duk wata huldar diflomasiya da Isra’ila, yana mai kiran Firaminista Benjamin Netanyahu a matsayin “mai kisan kiyashi”.
Shugaban na Colombia na bayyana cewa kama daga gobe Alhamis kasarsa za ta katse duk wata hulda Isra’ila ,shugaban na Colombia bangaren hagu na farko a tarihin kasar da ya dau irin wannan mataki, ya na mai fadar haka ne a wani jawabi ga magoya bayansa a babban birnin kasar Bogota.
Shugaban Colombia Gustavo Petro a jiya Talata ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” ga Falasdinawa a zirin Gaza, yana mai bayyana “cikakken hadin kai” tare da takwaransa na Brazil Luiz Inacio Lula Da Silva.
Shugaban Brazil cikin fushi y ana mai cewa “a Gaza, an yi kisan kare dangi. Dubban yara da mata da tsoffi ne ake kashewa.
Shugaban na Colombia ya bayyana cikakken goyon bayan ga Shugaban Brazil wanda a makon da ya gabata ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” ga Falasdinawa a zirin Gaza.