Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiTurkiyya zata shiga shari'ar da Africa ta kudu keyi da Isara'ila kan...

Turkiyya zata shiga shari’ar da Africa ta kudu keyi da Isara’ila kan kisan kiyashi a Gaza.

Date:

Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya ce kasar za ta haɗa kai da Afirka ta Kudu a ƙarar da kasar ta kai gaban kotun duniya dangane da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza.

Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai bayan tattaunawa da ministan harkokin wajen Indonesia, Retno Marsudi a ma’aikatar, Fidan ya yi magana kan lamarin inda ya bayyana abubuwan da aka tattauna a yayin ziyararsu a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

Fidan ya ce a lokacin tattaunawarsa ta diflomasiyya da kasashen da suka amince da Falasɗinu a matsayin kasa, daga ciki har da kungiyar hadin-kan kasashen Musulmi ta OIC da ta tarayyar kasashen Larabawa, wasu daga cikin kasashen sun nuna shirinsu na daukar matsaya dangane da batun.

Fidan ya bayyana kasashen Nicaragua da Colombia a matsayin wadanda tuni suka ɗauki matsaya kan wannan shari’a, inda ya jaddada niyyar da Turkiyya ke da ita na shiga wannan shari’ar.

A yayin da yake sa ran samun ci gaba a shari’ar da ake yi a gaban kotun duniya, Fidan ya jaddada irin ƙoƙarin da Turkiyya ta jima tana yi domin shirya wa wannan matakin.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories