Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn gano sakacin jami’an soji 2 a harin kauyen Tudun Biri- Shalkwatar Tsaro

An gano sakacin jami’an soji 2 a harin kauyen Tudun Biri- Shalkwatar Tsaro

Date:

Binciken helkwatar tsaro ta kasa ya bankado sakacin jami’an soji 2, a harin kuskuren da ya hallaka masu taron Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Kakakin helkwatar, Edward Buba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai.

Ya ce zuwa yanzu, an kammala bincike kan harin na jirage marasa matuka, wanda ya hallaka dumbin fararen hula, da kuma jikkata wasu, kuma wadanda aka samu da sakaci za su fuskanci shari’a.

Sai dai, bai yi cikakken bayani dangane da abinda sakamakon binciken ya kunsa ba.

Premier Radio ta rawaito yadda harin ya auku a ranar 3 ga Disambar 2023, wanda rundunar sojin kasa ta dauki alhaki, tana mai bayyanashi a matsayin na kuskure.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...