Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMajalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Date:

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data dakatar da kamfanin raba lantarki KEDCO kan yankewa kwastamomi layukan su da dage transfoma ba tare da bayar da wa’adi ba.

Danmajalisa Mai wakiltar Kiru Usman Abubakar Tasiu ne ya bukaci hakan yayin Zaman Majalisar karkashin Jibril Isma’il Falgore.

Da yake gabatar da kudurin wakilin Kiru, Tasi’u, ya koka da yadda kamfanin Kedco ke kin samarwar da al’umma transfoma ko kin gyarawa idan ta lalace duk da cewa basu ke samarwa ba.

Ya kuma bukaci gwamnatin Kano ta tilastawa kamfanin ya mayar da layin wutar da ya saukewa al’umma musamman a yankunan Kiru, Bebeji da Karaye.

Da yake bada gudunmawa kan kudirin dan majalisa mai wakiltar Ungoggo, Aminu Sa’ad, ya ce ko a majalisa ta takwas data tara majalisar bukaci gwamnati tayi kira ga hukumar wajen gyara yadda take gudanar da aikin ta, Sai dai har kawo yanzu lamarin yaci tura.

Aminu Sa’adu ya ce akwai bukatar kamfanin na Kedco ya rinka biyan al’umma diyya na gaza biya musu bukatun su musamman rashin wuta.

Aminu Abdullahi Ibrahim

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...