Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMatatar man Dangote ta kara karya farashin man Dizel zuwa N940, dana...

Matatar man Dangote ta kara karya farashin man Dizel zuwa N940, dana jirgin sama zuwa N980.

Date:

Matatar Man Dangote ta kara karya farashin litar man dizel zuwa N940, da farashin man jirgin sama zuwa N980.

Ragin farashin na zuwa ne kimanin mako biyu da kamfanin ya rage farashin litar man dizel zuwa N1,000 daga N1,200.

Kamfanin ya sanar da cewa masu sayen lita miliya zuwa sama a matatar ne za su samu a kan N940, amma masu lita 5,000 zuwa sama kuma a zasu sayi diesel din akan N970.

Kakakin rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya ce saukin da aka samu na daga cikin yunkurin kamfanin na ganin an samu saukin rayuwa da na kayayyaki a kasarnan.

Matatar Man Dangote ta kulla yarjejeniya da Kamfanin Man MRS don ganin jama’a suna samun mai a farashi mai sauki a gidajen man MRS a fadin kasarnan.

Ya kara da cewa za a fadada yarjejeniyar zuwa wasu manyan kamfanonin mai da ke da sha’awar hakan.

Karo na uku ke nan da Dangote ke rage farashin man dizel; daga N1,700 zuwa N1,200 zuwa N1,000 sannan zuwa N940, wanda Shugaba Bola Tinubu ya jinjina wa kamfanin.

Shugaban kungiyar masu masana’antu ta kasa (MAN), Ajayi Kadiri, ya yaba wa kamfanin Dangote yana mai cewa hakan na nuna kamfanonin cikin gida za su iya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

 

 

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...