Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar EFCC ta kama tsohon Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika bisa...

Hukumar EFCC ta kama tsohon Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika bisa zargin halatta kudin haram.

Date:

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika bisa zargin hallata kudin haram sama da naira biliyan takwas.

Jaridar Punch ta rawaito cewa ministan ya isa ofishin EFCC dake Abuja a da misalin karfe daya na rana a talatar nan inda ya amsa tambayoyi game da kwantiragin da ya bawa kamfanin Engirios Nigeria Limited mallakin kanin shi Abubakar Sirika.

Wata majiya ta bayyana cewa hukumar na bincike akan hadin bakin da sirika yayi da kanin sa wajen karkatar da kudi sama da biliyan 8 na ma’aikatar jiragen sama ta kasa.

Tuhumar da akewa sirika ta hada da hadin baki, cin amanar aiki, karkatar da kudaden gwamnati da Karin kudin kwantiragi, cin amana da hallata kudin haram yayin da yake shugaban tar ma’aikatar sufurin jiragen saman.

Tuni hukumar ta kama kanin nasa Abubakar sirika akan wannan badakala domin bincike ya tabbatar da ya karbi kudin aikin amman kawo yanzu bai kaddamar da aikin ba.

Majiyar ta tabbatar da an kama Abubakar sirika a ranar 4 ga watan Fabrairu kuma yana tallafawa hukumar a binciken yayan nasa da take.

 

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...