Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaMajalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Lantarki, don amsa tambayoyi game da ƙarin wutar lantarki.

Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Lantarki, don amsa tambayoyi game da ƙarin wutar lantarki.

Date:

Majalisar Dattawa ta gayyaci ministan lantarki, Adebayo Adelabu, da manyan jami’an hukumar lantarki ta kasa su gurfana gabanta domin amsa tambayoyi game da karin kudin lantarkin da aka yi.

Shugaban kwamitin majalisar na harkokin lantarki, Sanata Enyinnaya Abaribe, da ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki a ma’aikatar lantarki ta kasa a Abuja, ya ce majalisar ta riga ta bayar da iznin fara bincike, inda manyan hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi.

Mr Abaribe da kwamitinsa, sun nuna damuwa game da yadda ake fama da matsalar lantarki a kasar nan, inda suka ce lokaci ya yi da ya kamata a dauki mataki.

Minista Adebayo Adelabu kuma, ya lissafa kalubalen da ya shafi bangaren wutar lantarki, da ya hada da karancin kudi, barna, da rashin makamashin gas, da sauransu, sannan ya bukaci kwamitin ya ba ma’aikatar lantarkin goyon baya domin cimma nasarar gudanar da aikin da aka dora mata.

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...