Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaAkwai wasu ƴan bindigar da Gwamnati ta samu fahimtar juna dasu:Malam Nuhu Ribadu.

Akwai wasu ƴan bindigar da Gwamnati ta samu fahimtar juna dasu:Malam Nuhu Ribadu.

Date:

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya ce akwai wasu daga cikin ‘yan bindigar da gwamnati ta samu fahimtar juna da su.

Ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya na aiki wajen kawo karshen ta’addanci, ko da ya ke ba fitowa fili ake domin bayyana matakan da ake dauka ba.

Nuhu Ribadu, ya ce akwai sauye-sauye da aka samu da dama, musamman na adadin mutanen da ake kashewa a kasar nan kowanne wata, kuma an samu nasarar kashe wasu da dama daga cikin shugabannin ‘yan bindiga, da suka hada da Ali Kachallah, da ya jagoranci harin jami’ar Gusau, da aka sace dalibai, da Boderu, da Damina, da Dangote, da dai sauransu.

Ya ce an samu ci gaba a harkar tsaro a ƙasar nan, idan aka yi la’akari da yadda yanzu mutane ke zuwa duk inda suke so ba tare da fargaba ba.

Matsalar hare-haren ‘yan bindiga dai ta zama wani karfen kafa a yankin arewa maso yammacin kasar nan, inda ta ke ci gaba da jefa jama’a cikin tsaka mai-wuya a garuruwa da dama, musamman na yankin karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...