Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiTa'addanci babbar masifa ce da aka shigo da ita kasar nan: Shugaba...

Ta’addanci babbar masifa ce da aka shigo da ita kasar nan: Shugaba Bola Tinubu.

Date:

Shugaba Bola Tinubu ya ce ta’addanci babbar masifa ce da aka shigo da shi kasar nan, da kuma ya zama wata annoba ga nahiyar Afirka.

Ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar wajen buɗe babban taron yaƙi da ta’addanci na kasashen Afrika na yini biyu a Abuja, inda ya kara da cewa, ana kashe dubban milyoyin kuɗi wajen sayen makaman yaƙi da ‘yan ta’adda, da ya kamata a yi amfani da su wajen kula da lafiya da ilmi da samar da abubuwan more rayuwa a nahiyar a duk shekara.

Shugaba Tinubu ya ce, ‘yan ta’adda na neman ƙarfafa son zuciya a nahiyar, da ma kawar da mulkin dimokuraɗiyya, da haddasa cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, da harkokin tattalin arzikin ƙasashe da dama.

Saboda haka shugaban kasar ya bukaci takwarorinsa na ƙasashen Afrika su magance talauci, tare da inganta ilmi, ba ya ga yaƙi da ta’addanci.

Haka-zalika Tinubu ya buƙaci shugabannin kasashen Afrika su mayar da hankali kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, da ake amfani da su wajen samun kuɗin ta’addanci.

Shi ma mataimakin babban sakatare a ofishin yaki da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya, Vladimir Voronkov, ya ce taron na da nufin magance matsalar ta’addanci da ke ƙara ƙamari a nahiyar.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...