Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiDan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Date:

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai ziyara ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji domin yabawa hukumar kan tuhumar da take yiwa iyayensa.

Abdulaziz Ganduje ya ce zai taimaka wajen bayar da bayanai kan binciken da ake yiwa mahaifinsa na cin hanci da rashawa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Abdulaziz ya kai ziyarar ce domin yabawa Muhuyi a kan kokarinsa tare da goyan bayan tuhumar da ake yiwa mahaifinsa Ganduje da mahaifiyarsa da kuma dan uwansa.

Daily Nigerian ta ce bayanai masu sahihancin da ta samu sun shaida mata cewar, bayan yabawa da tuhumar da ake yiwa iyayen na sa, ya kuma bayyana damuwa a kan yadda aka cire sunan sa ba bisa ka’ida ba a matsayin darakta daga daya daga cikin kamfanonin da ake kara bada sanin sa ba.

A korafin da ya gabatar, Abdulaziz ya bayyana cewar wani mai harkar gine gine ya tintibe shi domin taimaka masa sayen filaye a Kano tare da masa tayin dubban daloli da kuma kamisho na naira miliyan 35.

Jaridar tace shi Abdulaziz ya mika kudaden da aka canja zuwa daloli ga mahaifiyarsa, amma abin takaici bayan wata 3 sai wanda ya biya kudin ya gano cewar an sayarwa wasu mutane daban filayen, saboda haka ya bukaci a mayar masa da kudaden sa.

Ziyarar tasa na zuwa ne awanni bayan da babbar kotun jihar Kano mai lamba 4 ta zauna domin fara sauraran shari’ar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan da uwargidansa Hafsat da ‘dan su Umar Abdullahi Umar da kuma wasu mutane 5 da ake tuhuma da laifuffuka guda 8 da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma karkata dukiyar jama’a.

Rahotannin sun ce Abdulazeez ya goyi bayan gurafanar da mahaifinsa a gaban kotu bisa zargin cin hanci da rashawa.

Rahotanni sun ce Abdulazeez ya nuna ɓacin ransa kan cire sunansa da mahaifinsa ya yi, ba tare da izininsa ba daga cikin daraktocin daya daga cikin kamfanonin da a ke zargi da handame kudaden al’umma.

Sai dai alkalin kotun, mai sharia Usman Na’abba, ya ce rashin ba su sammaci ya kawo tsako ga shirin da gwamnatin Kano ta yi na gurfanar da su.

Idan za a iya tunawa dai, a shekaru biyun da suka gabata Abdulaziz ya gurfanar da mahaifiyarsa Hafsat Ganduje a gaban kotu.

Latest stories

Related stories