Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3 ya ja hankalin shugabanni kan samar da kaykkawar makoma ga yan najeriya.
Muhammad Sa’ad ya bukaci hakan ne yayin taron cika shekara 5 da nadin Justice sidi bage Muhammad a matsayin Sarkin Lafiya a jiya Asabar.
SarkinMusulmin yace a halin yanzu al’ummar kasar nan na bukatar dawowar cigaba ta bangarori da dama cikin gaggawa.
Yace saboda haka akwai bukatar shugabanni a matakai daban daban sum aida hanaklai wajen magance matsin tattalin arziki da rashin tsaro da ake fuskanta a kasar nan.
A jawabin sa Shehun Borno Ibn Umar Garbai ya bukaci al’ummar kasar nan su rika bayar da sahihan bayanai kan ayyukan yan bindiga a arewa maso gabas da wasu sassan kasar.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Sarakunan Kano da na Zazzau da gwamnan JIhar Nasarawa da sauran manyan baki.