Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAtiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai...

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Date:

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan jam’iyyarsa ta PDP ne za su yanke shawararar makomarsa, a zaben 2027 mai zuwa.

Yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugaban kasa mai zuwa.

Atiku na wannan jawabi ga manema labarai bayan wata ganawa da aka ga ya yi da manyan jagorori da yan Takara shugaban kasa na wasu jamiyyu a kasar nan.

Daga cikin wadanda Atiku ya gana da su a baya-bayannan akwai dan takarar shugaban kasa a jam’iyyr LP, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bokola Saraki da jigo a PDP kuma tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

Tsohon Dantakarar mataimkain shugaban kasar Atiku Abubakar, yace ganawar tasu wani bangare ne na dunkulewa wuri guda tare da nuna adalci da kuma rashin nuna banbamci, wajen zabar shugaba na gari da zai kawo daidaito ga al’ummar kasar nan.

Latest stories

Related stories