Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin tarayya ta nada Aminu Dabo a matsayin shugaban kwamitin zartarwa na...

Gwamnatin tarayya ta nada Aminu Dabo a matsayin shugaban kwamitin zartarwa na kwalejin fasaha ta Gombe.

Date:

Gwamnatin tarayya ta nada sabbin shugabannin kwamitocin zartarwa na jami’o’in kasar nan da kwalejojin ilmi da na fasaha.

Nadin shugabancin ya shafi jami’o’I 50 da kwalejojin ilmi 37 da na fasaha 24.

Daga jihar Kano gwamnatin tarayyar ta nada Alh. Aminu Dabo a matsayin shugaban Kwamitin zartarwa na kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya dake Gombe.

A jami’ar Bayero kuwa an nada Sanata Udoma Udo Udoma, shugaban kwamitin zartarwar.

Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ABU, an nada Alh. Yayale Ahmad a matsayin shugaban kwamitin zartarwar jami’ar.

Sai jami’ar ilmi ta tarayya dake nan Kano da aka fi sani da FCE, inda aka nada Barr. A.U Mustapha SAN a matsayin shugaban kwmaitin zartarwa.

Ita kuwa kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya dake Kabo a nan Kano an nada mata Sir. Pual C. Chukwuma a matsayin shugaban kwamitin zartarwa.

FEDERAL MINISTRY OF EDUCATION1

Latest stories

Related stories