Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumi"Nan da watan yuni Najeriya bata bukatar shigo da mai daga ketare"-...

“Nan da watan yuni Najeriya bata bukatar shigo da mai daga ketare”- Dangote.

Date:

“Nan da watan yuni Najeriya bata bukatar shigo da mai daga ketare”- Dangote

Babban attajirin nan na Afrika Aliko Dangote ya ce zuwa cikin watan yuni kasar nan bata bukatar ta shigo da mai daga kasashen ketare.

Dangote ya ce matatarsa zata iya samarwa da kasashen Afrika ta yamma man fetur da diesel daidai da yadda yankin ke bukata.

Ya fadi haka a wani taron mamallaka kamfanoni na Afirka da aka yi a Kigali babban birnin Ruwanda ranar juma’a kan batun da ya shafi hanyoyin samar da makamashi.

Dangote ya ce Najeriya ba ta bukatar shigo da mai kamar na Fetur daga nan da makwanni 4 zuwa 5. Ya kuma bayyana cewar suna aiki tukuri a matatar Dangote domin ganin nahiyar Afrika ta tsaya da kafafunta a fannin makamashi.

Ya ce suna da wadataccen fetur da zai wadatar da yankin Afrika ta yamma baki daya da kuma man diesel da zai wadatar da Afrika ta yamma har da Afrika ta tsakiya, da ma man jirgin sama da zai wadatar da nahiyar Afrika baki daya har ma a fitar da shi zuwa kasashen Barazil da Mexico.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...