Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGagarumar ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutane 60 tare da jikkata wasu a Brazil.

Gagarumar ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutane 60 tare da jikkata wasu a Brazil.

Date:

Gagarumar ambaliyar ruwa da ta auku a kudancin jihar Rio Grande do Sul a kasar Brazil ta kashe mutane akalla 60 yayin da wasu 101 suka bace, kamar yadda alkaluman hukumomin yankin suka bayyana a ranar Lahadi.

Akalla mutane 155 ne suka jikkata, yayin da barnar da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ta tilastawa mutane fiye da 80,000 barin gidajensu. Kimanin mutane 15,000 sun fake a makarantu, da wuraren motsa jiki da sauran wasu matsugunan wucin gadi.

Ambaliyar ta haddasa barna sosai, ciki har da zabtarewar kasa, da lalata tituna da kuma gadoji a fadin jihar.

Jami’ai sun bayar da rahoton katsewar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa. Mutane sama da 800,000 sun rasa hanyar samun ruwan sha, a cewar hukumar kare farar hula ta kasar, wacce ta ambaci alkaluman kamfanin samar da ruwa na Corsan.
Da yammacin ranar Asabar, mazauna garin Canoas sun sami kansu cikin ruwa mai tabo shan kai, sun yi ta gwagwarmayar kwashe mutane a cikin kwale-kwale don kai su mafaka, kamar yadda wani bidiyo da kafar yada labarai ta UOL ta yada.

Ruwan kogin Guaiba ya kai tsayin mita 5.33 da karfe 8 na safiyar Lahadi agogon kasar, yawan ruwan da ya zarta wanda aka gani a lokacin ambaliya ruwa na tarihi ta auku a shekarar 1941, lokacin da tsawon ruwan kogin ya kai mita 4.76.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...