Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar sojin ƙasar nan ta hallaka ƴan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja.

Rundunar sojin ƙasar nan ta hallaka ƴan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja.

Date:

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka ƙaddamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen ‘yan bindigar.

Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun ƙasar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno.

Ya ce dakarun sojin ƙasar sun ga ‘yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su.

Haka kuma sojojin sun ce sun kuma samu nasarar kai hari a ƙauyen Allawa da ke kusa da Shiroro a jihar Neja, inda aka kashe ‘yan bindiga masu yawa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...