Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiWasu 'ƴan kasuwar ƙasar China sun sauka a Kano don zuba makudan...

Wasu ‘ƴan kasuwar ƙasar China sun sauka a Kano don zuba makudan kuɗi a fannin sarrafa shinkafa.

Date:

Wasu yan kasuwar kasar China sun sauka a jihar Kano domin zuba makudan kudi a fanin sarrafa shinkafa.

Da yake jawabi kwamashinan kasuwanci na jihar ann Adamu Aliyu Kibiya ya ce, zuwan ‘yan kasuwar na China daya ne daga cikin nasarorin gwamantin jihar na janyo masu zuba jari ‘yan kasashen waje.

Kwamanshinan masana’antun na jihar Kano ya ce a shirye gwamnati take ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ga ‘yan kasuwa na cikin gida da na kasashen waje.

Ya shaidawa ‘yan kasuwar ta kasar Sin cewa jihar Kano jiha ce mai zaman lafiya da albarkatun kasa wadanda ake matukar bukata a kasuwannin duniya.
A jawabin sa jagoran ayarin ‘yan kasuwar Mr. Diao Shengyun ya ce sun zo jihar Kano ne domin duba hanyoyin zuba jari a bangarorin masana`antun sarrafa shinkafa da na samar da takin zamani kana da na samar da injinan aikin gona na zamani.

Ya ce tuni suka yanke shawarar assasa kamfanin sarrafa shinkafa na buliyoyin naira a jihar Kano, domin tallafawa kokarin gwamantin jihar ta Kano wajen samar da wadataccen abinci
Mr. Shengyun ya ce a cikin tawagar tasu akwai shugabannin kamfanoni da kuma ‘yan kasuwa wadanda dukkannin su sun gamsu da saka jarin su a wadannan bangarori guda uku domin cin moriyar kowanne bangare.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...