Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKotu ta yankewa tsohon manajan bankin FCMB ɗaurin shekara 121.

Kotu ta yankewa tsohon manajan bankin FCMB ɗaurin shekara 121.

Date:

Wata kotu a jihar Anambra ta yankewa tsohon manajan bankin FCMB, Nwachukwu Placidus, hukuncin ɗaurin shekara 121 saboda samunsa da laifin zambar kuɗi.

Kotun ta samu tsohon manajan da laifin karkatar da wasu kuɗi kimanin naira miliyan 112.1 da wani kwastoma ya kawo da nufin sanya masa a asusunsa.

Cikin wata sanarwar da Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa ta kasa EFCC, ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce an gurfanar da mista Placidus a gaban kotun ne ranar 27 ga watan Maris ɗin 2018.

An tuhume shi da laifuka 16 da suka haɗa da sata da yin ƙarya a furucinsa da kuma a takardu.

Sanarwar ta ce a lokacin da Placidus ke aiki a matsayin manajan bankin FCMB reshen birnin Onitsha, ya karɓi kuɗi daga wani kwastoman bankin da nufin sanya masa kudin a susun ajiyarsa, amma sai mista Placidus ya karkatar da su.

Bayan gudanar da bincike ne, EFCC ta gano cewa Placidus ya karkatar da kuɗin domin amfanin kansa, inda kuma ya gabatar da takarda ta ƙarya da ke nuna shaidar saka kuɗin a asusun kwastoman, kan hakan ne kuma kotun ta ɗaure a gidan gyaran hali.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...