Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiIsra'ila ta bada sanarwar faɗaɗa yakin ta na kai hari birnin Rafah.

Isra’ila ta bada sanarwar faɗaɗa yakin ta na kai hari birnin Rafah.

Date:

Ga masu bibiyar abinda yake aukuwa a Gabas ta Tsakiya musamman yaki tsakanin Israila da Palestinawa, yau ta zama ranar bakin ciki saboda Israila ta bada sanarwar fadada yakin ta shirin kaiwa birnin Rafah farmaki.

A wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau, Israila ta bukaci yan Palestinu da azabar yakin Gaza ta tilasta musu neman mafaka a birnin Rafah, da subar birnin, cikin yan awanni, dalilin shirinta na kawo farmaki da sakin bomabomai a birnin.

Majalisar Dinkin Duniya da Shugabanni na manyan kasashe da dama sunyi ta roko da jawo hankalin Shugaban Israila Benjamin Netanyahu da ya dakatar da shirin nasa na afkawa Rafah saboda gudun kisan kiyashin da harın zai haifar amman Israila tayı biris da rokon nasu.

Birnin Rafah dai gari ne na yan gudun hijira musamman ma mata da kananen yara da yawansu yakai miliyan daya da rabi.

A watannin da suka wuce Israila tayi rugurugu da Birnin Gaza inda ta kashe Palestinawa kusan 400,000 wadanda kashi saba’in cikin dari daga cikinsu matane da kananen yara kuma ta tilastawa mutane sama da miliyan daya da suka rasa matsugunnin su da tserewa neman mafuka a Rafah da sauran gurare.

Yau ne Benjamin Netanyahu ya bada sanarwar cewa dük mai son ransa ya kauracewa Birnin Rafah don sojojin Israila sunyi shirin shiga su mamaye birnin. Tuni rahotanni har sun fara fita cewa wani bom da Israila ta saki da safen nan a wannan birni yayi sanadin mutuwar yara 4 da jikkata mutane da dama.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...