Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƳan sandan Isra'ila sun kai sumame Otal din da gidan talabijin din...

Ƴan sandan Isra’ila sun kai sumame Otal din da gidan talabijin din Al-Jazeera ke amfani da shi a gabashin birnin Jerusalem.

Date:

‘Yan sandan Isra’ila sun kai samame Otal din da gidan talabijin din Al Jazeera ke amfani da shi a gabashin birnin Jerusalem a matsayin ofishinsa na yada shirye-shirye, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya tabbatar a Lahadin nan.

Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan Intanet, ya nuna jami’an tsaron cikin fararen kaya suna lalata naurorin daukar hoto na Al Jazeera a Otal din, biyo bayan umarnin majalisar ministocin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na haramtawa Al Jazeera yada shirye-shirye a kasar, sakamakon zargin zama barazana ga tsaron kasar.

Gidan talabijin din na Al Jazeera ya musanta zargin yana mai cewar labari ne maras tushe balle makama, kuma wannan wani yunkuri ne kawai da Isra’ila ke yi wajen kara jefa rayuwar ‘yan jarida cikin hatsari.

Kafar yada labaran Al Jazeera ta yi kaurin suna wajen sukar yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, kuma tana ci gaba da yada labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa game da yakin, ba dare da rana.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...