Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumomin Nijar sun bada umarnin rufe wuraren haƙar Gwal hudu a ƙasar.

Hukumomin Nijar sun bada umarnin rufe wuraren haƙar Gwal hudu a ƙasar.

Date:

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bada umarnin rufe wuraren hakar Gwal guda hudu na kasar da ke karkashin kamfanin kasar Chaina, bayan mutuwar dabbobi masu tarin yawa da suka sha gurbataccen ruwan dagwalon da ke fitowa daga kamfanin.

Ma’aikatar kula da ma’adanan kasar ce dai ta bada umarnin rufe kamfanin na kasar Chaina mai suna Sahara SARL, bayan ziyarar gani da ido, bisa rakiyar jami’an ‘yan sanda da ke binciken lamarin.

Tun a cikin watan Janairun da ya gabata ne dai kamfanin ya fara aikin hakar Gwal a yankin.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun jima suna kokawa da yadda kamfanin hakar Uranium na Faransa Orano da ake kira Areva a da ke gurbata muhalli a kasar, bayan ya shafe shekaru sama da 40 yana aikin hakar ma’adanan a arewacin Jamhuriyar Nijar.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...