Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnati zata duba yiwuwar soke dokar hukunci ga masu yunƙurin kashe kansu.

Gwamnati zata duba yiwuwar soke dokar hukunci ga masu yunƙurin kashe kansu.

Date:

Gwamantin tarayya zata duba yiwuwar soke dokar nan da ta tanadi hukunci ga wanda yayi yunkurin kashe kansa.

Babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a Prince Lateef Fagbemi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa kan sadarwa da hulda jama’aa ofishin ministan Kamaruddeen ogundele ya fitar.

Ministan ya bayyana haka yayi da yake karbar tawagar Asido faoundation wata kungiya dake wayar da kai kan lafiyar kwakwalwa da yaki da tsangwama da ake nunawa masu lalurar.

Shugaban kungiyar na kasa Dr Jibril Abdulmalik ya nemi hadin kan ma’aikatar sharia’a domin sake Nazari kan dokar hukunta masu yunkurin kashe kansu, tare da tabbatar da aiki da sabuwar dokar kula da lafiyar kwakwalwa da tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya samar a janairun 2023.

Dr Abdulmalik yace bincike ya nuna cewa kashi 80-90 cikin dari na mutanen dake yunkurin hallaka kansu na fama da matsalar kwakwalwa ko kuma cutar damuwa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...