Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiManyan Arewa sun gargadi Tinubu kan bawa Amurka da Faransa damar kafa sansanin soji.

Manyan Arewa sun gargadi Tinubu kan bawa Amurka da Faransa damar kafa sansanin soji.

Date:

Wasu manyan Mutane daga nan Arewa sun gargaɗi gwamnatin tarayya kan ba wa Amurka da Faransa damar kafa sansanin soji a kasar nan bayan korarsu da aka yi a yankin Sahel.

 

Cikin wata wasiƙa da suka aikewa shugaban kasa Bola Tinubu da kuma shugabancin Majalisun ƙasar nan a ranar Juma’a, shugabannin sun ce kada gwamnatin tarayyar ta sake bayar da kai bori ya hau.

 

Cikin waɗanda suka sanya hannu kan wasiƙar akwai Farfesa Abubakar Siddique Mohammed na Cibiyar Ci gaban Dimokradiyya da bincike da ba da horo ta (CEDDERT), da ke Zaria, da Farfesa Kabiru Sulaiman Chafe tsohon Ministan mai, da Farfesa Attahiru Jega tsohon shugaban INEC da Farfesa Jibrin Ibrahim na CDD da Auwal Musa Rafsanjani shugaban (CCISLAC) sai kuma Y. Z. Ya’u na CITAD.

 

Wasiƙar ta yi zargin cewa gwamnatocin Amurka da Faransa na kamun kafa wajen Najeriya da kuma wasu ƙasashe da ke mashigar tekun Guinea, tare da samar da wata yarjejeniya da za ta basu damar sake tsugunar da dakarunsu da aka kora daga Mali da Burkina Faso da kuma Nijar a yankin.

 

Waɗanda suka aike wasiƙar sun nuna damuwa kan cewa Najeriya na wani mataki ne da yake mai hadari tsakanin ƙasashen yakin mashigar tekun Guinea, idan ta bayar da kai bori ya hau hakan zai iya jefa tsarin tsaronta na cikin gida cikin hadari.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...