Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn gano cewa Tinubu ya wuce Landan daga birnin Riyadh

An gano cewa Tinubu ya wuce Landan daga birnin Riyadh

Date:

Kwanakin shida tin bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya halarci taron tattalin arzikin a birnin Riyadh na Saudiyya har yanzu bai dawo nan Najeriya ba.

Taron na kwanaki biyu da ya tattauna kalubalen da zuba jari ke a bangaren gwamnati da yan kasuwa, a bude shi a ranar Lahadin makon jiya aka karkare a ranar Litinin.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, kan dalilin da ya sa har yanzu Tinubu bai dawo nan Najeriya ba.

Wannan dai ya janyo fara yada jita-jitar cewa, ko shugaban ya tafi kasar Faransa ne, kasar da ya sha zuwa a baya domin a duba lafiyarsa.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ce wata majiya ta tabbatar mata da cewa, Tinubu ya tafi zuwa London daga birnin Riyadh din na Saudiyya.

Jaridar ta ce ai shaida mata cewa Tinubu ya je London din ne domin wata ziyara ta kashin kai.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...