Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAPC bata da niyar mayar da Najeriya tsarin jam'iyya daya-Jigon jam'iyyar.

APC bata da niyar mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya-Jigon jam’iyyar.

Date:

Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Bashiru, ya ce shugabannin jam’iyyar ba su da niyyar mayar da kasar nan kan tsarin jam’iyya daya, illa ganin sun gina jam’iyyar domin ci gaba da lashe zabe.

Ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga dimbin magoya bayan jam’iyyar da suka halarci sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja tare da nuna goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, inda suka nemi kada ya sauka daga mukaminsa.

Dakatar da Ganduje da wasu shugabannin jam’iyyar biyu na mazabarsa suka yi a baya-bayan nan, ya haifar da zanga-zanga, inda mutanen yankin arewa ta tsakiya suka yi kiran ya yi murabus.

Amma da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa, Ganduje ya ce wadannan mutane na fargabar irin kokarin da jam’iyyar ke yi, saboda a cewarsa tuni sun san 2027 tasu ce, ba su da wani katabus.

Sai ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar APC su yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wasan yara, inda ya ce, sun fahimci abinda suke yi.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...