Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiEFCC ta nesanta kanta daga wani jerin sunan tsoffin gwamnoni.

EFCC ta nesanta kanta daga wani jerin sunan tsoffin gwamnoni.

Date:

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziƙi ta ta’annati ta EFCC ta nesanta kanta daga wani jerin sunaye wanda ke yawo a wasu jaridu da kafafen sada zumunta da ke cewa tana bincikar wasu tsofaffin gwamnoni kan zargin rashawa.

A jiya Asabar ne wani labari ya rika yawo kan cewa akwai tsofaffin gwamnoni 58 waɗanda hukumar ke bincika kan zargin almundahana ta kimanin Naira tiriliyan 2 da biliyan 187 a cikin sama da shekara 25.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC Dele Oyewale ya fitar a yau Lahadi, ya bayyana rahotannin a matsayin na karya.

Oyewale ya bayyana cewa wadanda suka ƙirƙiri jerin sunayen su kaɗai suka san manufar da suke son cimma.

Sai dai a yan kwanakin da suka gabata hukumar ta EFCC ta yi ta bincikar wasu tsofaffin gwamnoni daga ciki har da tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello inda take zarginsa da cire dala miliyan 720 daga asusun jihar domin biyan kuɗin makarantar dansa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...