Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiManoman tumatir na kokawa kan mummunar asara

Manoman tumatir na kokawa kan mummunar asara

Date:

Manoman tumatir a jihar Katsina na kokawa kan yadda za su dawo da kudin da suka zuba a noma, sakamakon faduwar tumatirin a ’yan kwanakin nan.

Manoman sun ce sun kashe makudan kudi wajen sayo injinan ban-ruwa da na kashe kwari da taki da sauransu.

Malam Halliru Sani, wani manomi ne a garin Tafoki da ke Karamar Hukumar Faskari, ya ce, a wannan shekara, abin da suke sa rai shi ne samun kudade masu yawa, inda manoma da dama suka kauce wa noman saboda rashin jari.

Ya danganta matsalar da son-kai na dillalan tumatir da sauran dillalai, wadanda a cewarsa, a koyaushe suna hada kai da manoman gida.

Wani manomi a Funtuwa, Malam Shu’aibu Aminu ya ce, da yawa daga cikinmu sun yi asara, bayan mun yi fama da cutar da ta kusan lalata amfanin gonakinmu.

Ya shawarci manoma dsu daina noman amfanin gona guda daya domin kare dimbin jarin da suke zubawa.

Daya daga cikin dillalan tumatir a garin Danja, Malam Hamza Idris ya ce, manoma a koyaushe suna neman hanyar dora laifin a kan dillalai, musamman idan farashin kasuwa bai yi musu dadi ba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...