Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHarsashin bindiga a fadar gwamnatin Kano ya jikkata ɗan jarida a ranar...

Harsashin bindiga a fadar gwamnatin Kano ya jikkata ɗan jarida a ranar ƴancin ƴan jarida ta duniya.

Date:

Dan jaridar dake aiki da gidan talabijin na jihar Kano ARTV mai suna Nazirun Idris Ya’u ya tabbatarwa da Premier Radio faruwar lamarin, sai dai ya ce ba’a san daga inda aka harbo harsashin bindigar ba.

Ya kara da cewa harsashin ya masa rauni amma ba mai yawa ba, kuma tuni jami’an yan sanda a fadar gwamnatin Kano suka kaddamar da bincike kan lamarin.

Kawo yanzu fadar gwamnatin Kano ba ta ce komai ba kan wannan Harbin bindiga da ya shafi dan jarida a fadar gwamnatin Kano.

Latest stories

Related stories