Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiA Makon Gobe Gwamnatin Tarayya Za Ta Bude Shafin Neman Rancen Kudin...

A Makon Gobe Gwamnatin Tarayya Za Ta Bude Shafin Neman Rancen Kudin Karatu Ga Dalibai.

Date:

Gwamnatin tarayya za ta bude shafin neman rancen kudin karatu a ranar Juma’ar makon gobe.

Babban daraktan asusun lamunin karatu na Najeriya (NELFUND) Akintunde Sawyerr ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis, mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai da hulda da jama’a na asusun, Nasir Ayitogo.

Ya ce an tsayar da ranar 24 ga Mayun 2024 a matsayin ranar bude shafin na neman rancen kudin karatun ga daliban manyan makarantun.

Ya ce masu buƙatar rancen za su iya shiga shafin ta www.nelf.gov.ng domin neman wani taimako ko kuma su tuntubi asusun ta info@nelf.gov.ng.

Ya ce shafin na da saukin sarrafawa, wanda ta cikin shi dalibai za su iya samun rance kudin makaranta ba tare da damuwa ba.

Babban daraktan ya shawarci wadanda suka cancanci neman rance su gaggauta cikewa domin morar tsarin.

Latest stories

Related stories