Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Date:

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki zagon kasa, Ola Olukayide, ya musanta zargin shi ne ya fara bincikar tsohon gwamnan Kogi, Yahya Bello.

A wata hira da manema labarai jiya a Abuja, shugaban na EFCC ya ce shi ma gadar binciken ya yi daga tsohon shugaban hukumar.

Ya kuma ce ba shi da wani dalilin yi wa Yahya Bello bi-ta-da-kulli, illa kishin ganin an samu ci gaba a kasar nan, musamman ganin yadda cikin wata shida da fara aiki a hukumar, aka samu damar kwato kudi naira milyan dubu 120 daga hannun ‘yan damfara.

Mr Olukayide, ya musanta cewa jami’ansu na aiki da son zuciya tun bayan da ya kama aiki a bara, kuma matukar ba su bibiyi shari’ar Yahya Bello ba, EFCC ba za ta iya bincikar kowa ba ke nan.

 

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...