APC ta ce shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu yana hutawa a Turai gabanin kama aiki gadan gadan bayan rantsuwa a 29 ga watan Mayu mai zuwa.
Sakataren yada labaran jamâiyyar na kasa, Felix Morka ne ya bayyana hakan a zantawarsa da kafar Channels.
Yace yanzu haka Tinubu na cikin koshin lafiya, kuma bayan sauke gajiyar zabe a Turai, zai dawo gida domin dorawa daga inda aka tsaya.
âTabbas yanzu yana turai, cikin koshin lafiya. Ya yanke shawarar zuwa hutun ne bayan gamawa da hidimar zabeâ, inji Morka.
âDa zararn ya dawo kuma ya karbi rantsuwa a 29 ga Mayu, babu sauran kakkautawa. Nauyin tafiyar da harkokin kasa irin Najeriya zai hau kansa. Na san yana gab da dawowaâ.
Morka ya kara da cewa bai wai iya hutun ne kadai ya kai Tinubu waje ba, aâa, har da batun tattaunawa da shugabannin kasashen da ragowar masu ruwa da tsaki, domin tsara hanyoyin cimma manufofin gwamnatin sa cikin saukI.
Rashin jin duriyar shugaban mai jiran gado, ya haifar da cece kuce tsakanin jamaâa musamman yan adawa, wadanda ke zargin Tinubun ya fita ne domin duba lafiyarsa, daya daga cikin abubuwan da ake ganin zasu hana shi mulki idan ya ci zabe.
