Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShariah da KotuBadakala: Majalisa ta gayyaci ministoci 2 | Premier Radio | 12.04.2023

Badakala: Majalisa ta gayyaci ministoci 2 | Premier Radio | 12.04.2023

Date:

Kwamitin Majalisar Wakilan kasar nan da ke bincike kan zargin batan gangar danyen mai miliyan 48 a ya gayyaci Ministocin Kudi da na Shari’a da wasu manyan shugabannin hukumomin kasar nan domin bayar da bahasi a game da zargin badakalar. 

Shugaban Kwamitin Binciken Mark Gbillah, ya ce ana zargin Ministar Kudi da karya dokar gwamnati ta tsarin fallasa masu yi wa gwamnati zagon kasa ta hanyar kin biyan masu fallasawar adadin kudin da ya dace a ba su.

Ya ce ana zargin Ministan Shari’a da karbar kudade daga ketare ba tare da sanyawa cikin asusun gwamnati ba.

Sai dai bai bayyana ranar da jami’an gwamnatin za su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi ba.

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ne Majalisar ta yanke shawarar fara bincike kan bantan miliyoyin gangar man, wadanda ake zargin wasu manyan jami’an gwamnatin da karkatarwa zuwa kasar China.

Latest stories

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Akwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a 2024-Bankin Duniya

Bankin Duniya ya ce akwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin...