Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Zamfara ta kara wa'adin gwamnatin shugabannin kananan hukumomi

Majalisar dokokin Zamfara ta kara wa’adin gwamnatin shugabannin kananan hukumomi

Date:

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsawaita wa’adin gwamnatin shugabannin kananan hukumomi da wasu kwanaki 45.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar Malam Nasiru Biya biki ya raba wa manema labarai juma’ar nan.

Ya ce ‘yan majalisar sun cimma matakin ne a zauren taron bayan sun samu bukatar tsawaita wa’adin aiki daga ranar 14 ga watan Afrilu zuwa 29 ga watan Mayu.

Shugaban majalisar, Farutenure Dosara ne, ya gabatar da bukatar gwamnati ga majalisar.

Sanarwar ta ruwaito Dosara na cewa bukatar ta fito ne daga hannun Gwamna Bello Matawalle ta ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...