Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso, Atiku da Obi Na Tattaunawa Domin Kafa Sabuwar Jam’iyyar MAJA, Don...

Kwankwaso, Atiku da Obi Na Tattaunawa Domin Kafa Sabuwar Jam’iyyar MAJA, Don Tinkarar zaben 2027

Date:

Masanin siyasar nan, Farfesa Part Utomi, ya ce ana tattaunawa tsakanin manyan yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 wato Atiku Abubakar na PDP, Petre Obi na LP da kuma Rabi’u Kwankwaso na NNPP domin samar da babbar jam’iyyar hadaka.

Da yake tabbatar da haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Utomi ya ce hakan wani shiri ne na samar da babbar jam’iyyar adawa mai karfi domin tunkarar kakar zabe mai zuwa a 2027.

Ya ce wannan wani yukuri ne na ceto kasar nan daga halin tasku da mulkin APC ya jefa ta wanda ya kira da mulkin azurta kai gawasu tsirarun mutane.

Utomi ya ce kasar nan na samun koma baya ne sakamakon rashin wata kwakwakwarar jam’iyya da za ta dora ta kan turbar da ta dace.

Ya ce “Na tattauna da Alhaji Atiku Abubakar, na tattauna da Engr. Rabiu Kwankwaso, na tattauna da Peter Obi, da ma wasu sauran mutane da za su iya samar da babbar jam’iyyar adawa ta hadaka.

Na fada musu wannan aiki ba don kashin kanku bane sai don ci gaban yan kasa, wannan aiki ne da zai shafi gamagarin dan Najeriya da ke yawo akan titi”.

“Muna neman hanyar da Najeriya za ta amfani kowa, akwai bukatar mu samar da jam’iyyar da za ta bijiro da matsalolin yan Najerya domin a magancesu.

Idan mukayi wannan yunkuri shi ne za a samu yan Najeriya da za su samar da shigabanci na gari, shugabancin da ba zai zama na arzurta kai ba wanda shi ne ke kassara siyasar Nijeriya, abinda muke bukata shi ne mutanen da za su sadaukar da kansu domin gina kasa”

Tin bayan kammala zaben 2023 ne ake ta rade-radin yin hadakar kafa jam’iyyar tsakanin manyan yan takarar shugaban kasa a zaben wanda kawo aka kasa cimma hakan.

Latest stories

Related stories