Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan Gwagwarmayar a fadin duniya za suyi taron nuna alhini kan kisan...

Yan Gwagwarmayar a fadin duniya za suyi taron nuna alhini kan kisan kiyashin da ake yiwa Falasdinawa

Date:

A yau Asabar ne yan gwagwarmaya da neman yanci daga sassan duniya gaba daya suka shirya gabatar da wani taron nuna alhininsu ga kisan kiyashi da mutanen falastine ke fuskantar a wajen israila.

Tarukan da za’ayi a sassan duniya ciki har da Najeriya, har ma da wani shiri na musamman a nan Premier Radio da zai zo muku bayan wannan labarai, bisa ta’addancin da Isra’ila ke aikatawa Falasdinawa.

Wannan na zuwa yayin da hukumomin lafiya a falastine ke cewa sama da mutane 23,000 ne suka rasa rayukansu a haren haren kan mai uwa dawabi da Isra’ila ke kaiwa tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Majalisar dinkin duniya tace yawancin wadanda suka rasa ransu mata ne da kananan yara, hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya unicef tace kashi 40 cikin dari na wadanda aka kashe yara ne da suka kama daga shekaru 18 zuwa kasa.

Bayan kisan kare dangi da take cigaba da aikatawa, kasar Israila ta kuma hana kungiyoyin bada agaji shiga yankin domin tallafawa wadanda ke tsananin bukatar taimako.

Tuni dai Ofishin jakadancin Falastine a Najeriya ya samar da asusu da al’umma zasu iya bada gudunmawa domin tallafawa al’ummar Falastine.

Ga masu son bada tallafin su da Naira zasu iya sakawa a asusu mai lamba 2019442840, masu niyyar bada tallafin da Dalar Amurka sai su sa a lambar 2006113227

A bankin First Bank, mai sunan Asusun Embassy of the State of Palestine.

 

Latest stories

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data kirkiri masarautun...

Related stories

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data kirkiri masarautun...