Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMajalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Date:

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data kirkiri masarautun Kano Hudu gyara.

Majalisar dokokin jihar Kano ta kira dokar Masarautun Kano domin yi mata gyara.

Majalisar ta amince da dawo da dokar data kirkiri masarautu hudu a jihar nan domin yi mata gyara yayin zamanta na Talatar nan karkashin Kakakinta Jibril Isma’il Falgore.

Hakan dai ya biyo bayan kudirin gaggawa da shugaban masu rinjaye na Majalisar kuma Wakilin Dala Lawan Hussaini ya gabatar kan batun.

Bayan gabatar da wannan bukata, kudurin ya samu goyon bayan wakilin karamar hukumar Dawakin Kudu Shu’aibu Rabi’u.

A wani labarin kuma majalisar ta bukaci gwamnati ta biyawa Daliban sakandire da suka fadi jarabawar Kwalafayin kudi domin samun damar rubuta jarabawar kammala sakandire SSCE.

Dan majalisa mai wakiltar Madobi, Sulaiman Mukhtar Ishaq, ne ya gabatar da kudirin.

 Aminu Abdullahi Ibrahim

Latest stories

Related stories