Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNijeriya ce ta farko a tattalin arzikin Africa a da, yanzu ta...

Nijeriya ce ta farko a tattalin arzikin Africa a da, yanzu ta dawo ta hudu.

Date:

Wani rahoton asusun lamuni na duniya, ya ce an samu sabon jadawalin ƙasashen da suka fi girman tattalin arziƙi a nahiyar Afrika, inda Nijeriya da ta taɓa zama ƙasar da tafi kowacce girman tattalin arziki yanzu ta sulmiyo zuwa ta huɗu, yayin da Afrika ta kudu ta ke sahun gaba.

Sai dai rahoton ya ce girman tattalin arzikin ƙasashen ba yana nuni da irin rayuwar da galibin al’ummarsu ke yi ba ne.

Ƙasashe da dama na ci gaba da fuskantar yawaitar bashi, da ƙalubalen kayan more rayuwa, da hauhawar farashi, da kuma koma-bayan tattalin arziki.

Asusun lamunin ya ce, matsalolin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, da suka haɗa da hauhawar farashi, da yawaitar cin bashi da matsalar rashin tabbas na gwamnatoci, na matuƙar shafar tattalin arziƙin ƙasashen Afirka.

Yanzun dai kasar Afrika ta kudu ce ta farko a fannin tattalin arziki, sai kuma Masar da ke biye mata.

Algeria mai ɗimbin albarkatun man fetur ce ta uku, yayin da Nijeriya da ta taɓa kasancewa giwar Afrika yanzu ta zama ta huɗu, sai kasar Habasha ta biyar.

Latest stories

Related stories