Saurari premier Radio
41.5 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciAkwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a 2024-Bankin Duniya

Akwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a 2024-Bankin Duniya

Date:

Bankin Duniya ya ce akwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a shekarar 2024 da muke ciki, inda zai karu da kashi 3.3 a wannan shekara da kuma kashi 3.7 a shekarar 2025.

Wannan na kunshe a wani rahoton bankin duniya na watan Janairun 2024.

Bankin Duniyan ya yi wannan hasashen ne tare da fatan tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke gudanarwa a kasa za su haifar da da mai ido. Duk da cewa, tana da tunanin za a samu koma bayan tattalin arziki a duniya, shekara uku a jere.

Rahoton ya nuna cewa, za a samu bunkasar tattalin arziki a wannan shekarar da kashi 3.3 zai kuma karu zuwa kashi 3.7 a shekarar 2025, kuma wannan na faruwa ne saboda ganin matakan bunkasar tattalin arzikin na da gwamnati ke yin a kara bayyana.

Haka kuma abubuwan da za su taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya a wannan shekarar sun hada da fitar da wasu kayyakin da ake sarrafawa a gida zuwa kasashen waje da kuma sake fasallin farashin kayayyaki a hankali ta yadda al’uimma za su shiga saye da sayarwa don bunkasa tattalin arzikin su.

To sai dai wannan na zuwa yayin da ake hasashen tattalin arzikin duniya zai yi kasa a karshen shekarar 2024, kamar yadda mujallar bankin duniya mai suna ‘Global Economic Prospects’ ta nuna.

Latest stories

Ýan Houthi sunyi iƙirarin kai hari kan wasu jiragen ruwa hudu.

'Yan Houthi na kasar Yemen, sun yi ikirarin kai...

Zamu kawo ƙarshen wahalar man fetur gobe laraba- NNPCL.

Kamfanin mai na kasa, ya tabbatar da cewa, gobe...

Related stories

Ýan Houthi sunyi iƙirarin kai hari kan wasu jiragen ruwa hudu.

'Yan Houthi na kasar Yemen, sun yi ikirarin kai...

Zamu kawo ƙarshen wahalar man fetur gobe laraba- NNPCL.

Kamfanin mai na kasa, ya tabbatar da cewa, gobe...