Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoBincike: Alummar Gainawa na fama da tsananin duhu sanadiyar rashin wutar lantarki

Bincike: Alummar Gainawa na fama da tsananin duhu sanadiyar rashin wutar lantarki

Date:

Yayin da alummar kwaryar birnin kano ke raba dare a waje suna tafiyar da alamuransu ba tare da fargabar na, tituna na walwali da hasken fitila tamkar rana garin Gainawa dake karamar hukumar Kura da zarar dare ya tsala basu da kwanciyar hankali domin tsananin duhun dake lulube garin.

Babu kyalin kwan fitila da ga cikin kowane gida balle ayi batun fitilar da zata haska titi. Binciken Premier radio ya tabbatar da tun da aka kafa garin yau shekaru 20 kenan basu taba samun wutar lantarki ba.

Duk da cewar sunaji suna gani kamfanonin dake gudanar da ayyukansu suka jawo wuta, polewire ta ratsa ta cikin garin su amman su ko oho.

Rashin wutar ya sanya harta ruwan amfani yayi wahalar samu domin saidai masu kudi su tashi inji su kunna borehole talaka kuwa saidai ya sai ruwa a hannu yan garuwa ko ya bi layi ya debi ruwan amfani a wani tankin ruwa dake amfani da hasken rana da wata kungiya mai zaman kanta ta samar a garin.

Wani dattijo da aka kafa garin na Gainawa a gaban idon sa ya bayyana mana cewa tun a wancan lokaci daman basu da wuta kuma har kawo yanzu da girma ya same su, watar nepa saidai su hango ta a makwabtan garuruwa.

Malam Yusha’u yace sun dawo garin ne daga garin sun na asali dake gadar tamburawa sanadiyar ambaliyar ruwa shekaru 20 baya.

Saidai tun sanda gwamnati ta kafa musu garin Gainawa ba a hada musu wuta ba.

Rashin wutar ya sanya karuwar rashin tsaro a yankin musamman kwace.

Imrana ya bayyana cewa da tsakar dare barayi suka tsallako gidan shi suka sace mishi awakin shi guda 24 wadanda sune hanyar cin abincin shi.

Yace tun bayan satar karin shi ya karye Kuma rayuwa tayi tsanani.

Rashin wutar lantarkin yana neman gurgunta kananan sana’oi a jihar domin dukkan masu sana’ar data shafi amfani da wuta sun fara kulle shagon su.Kadan daga cikin su da suka cije suka cigaba da sana’ar tsadar man fetur ya sanya sun fara karaya kamar yanda wani mai shagon chajin waya ya shaida mana.

Malam Abbas yace da kyar take iya samun riba da sana’ar saboda tsadar man fetur da kudin motar da take kashewa yazo cikin gari sayen man.

Farfesa Murtala sagagi na makarantar koyar harkokin kasuwanci ta Dangote dake BUK yace ashin wuta yana kwo tarnaki akan cigaban alummar yankin

Rashin wutar lantarkin yana neman tagayyara ilimin sama da dalibai 2000 dake halartar makarantar Gundutse chiki special primary school. Malami a makarantar Mahmud Adam ya shaida mana cewa gogewar daliban makarantar idan aka kamanta da ta takwarorin su dake karatu a makarantun cikin gari za’a samu matukar koma baya.

Abdullahi shuaibu gundutse shine kan gaba wajen fafutukar samar da wutar lantarki a garin ya kuma bayyana yanda suke tura wasikun neman taimako ga chairman din karamar hukumar Kura da yan majalisar tarayya da jiha da suka sauka a 2023 har ma da neman taimakon kamfanonin dake makwabtaka da su amman har yanzu hakansu bai cimma ruwa ba.

Saidai dana tuntubi chairman din karamar hukumar Kura Mustafa Abdullahi Rabiu game da matsalar yace bashi da masaniya akan rashin wutar domin kuwa yan garin basu taba zuwa sun kawo mishi kokensu ba.

Hukumar samar da wutar lantarki ta karkara REA ce keda alhakin samar da wuta ga alummar karkara kamar yanda sashe na 128 na dokar ya tanada.

Saidai masani a fannin lantarki Kunle Olubiyo yace kamata yayi gwamnatocin jihohi su tallafawa hukumar wajen magance matsalolin wutar da bai kai ya kawo ba kamar irin matsalar Gainawa da transformer da sauran kayan aiki kawai suke bukata a jono musu wutar

Shugaban hukumar samar da wutar lantarki ta karkara ta jihar Kano Engr Sani Bala Dambatta cewa yayi basu samu korafin alummar Gainawa a rubuce ba amman zasu bi diidigin alamarin.

Munyi kokarin jin ta bakin yan majalisa masu wakilitar Kura a matakin jiha da tarayya Yusuf Datti Kura da Alhassan Zakariya Ishaq amman hakanm u bai cimma ruwa ba.

 

 

 

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...