‘Yan Houthi na kasar Yemen, sun yi ikirarin kai hari kan wasu jiragen ruwa hudu, ciki har da na Amurka biyu, a tekun Bahar Maliya.
Kakakin rundunar, Yahya Sarea, a wani jawabi ta gidan talbijin, ya ce Yemen sun kai farmakin soja kan jiragen ruwan yaƙi da ke musu barazana a Bahar Maliya, inda harin jirage marasa matuƙa ya sauka kan jiragen ruwan yaƙin Amurka biyu, kuma an cimma nasara a manufar kai harin.
Yahya Sarea, ya kara da cewa, harin ya zo ne bayan da jiragen suka karya dokar hana zirga-zirga a tekun zuwa tashoshin ruwan Falasdinu da aka mamaye.
Sojojin Houthi dai sun kwashe tsawon watanni suna kai hare-hare kan hanyoyin jiragen ruwa, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa, daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kashe-kashe a Gaza.