Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiDavid Cameron ya ce an gabatarwa kungiyar Hamas tayin tsagaita wuta.

David Cameron ya ce an gabatarwa kungiyar Hamas tayin tsagaita wuta.

Date:

A halin da ake ciki kuma, sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Cameron, ya ce an gabatarwa kungiyar Hamas tayin yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana 40, tare sakin dubban Falasdinawan da Isra’ila ta kama a matsayin fursuna, bisa sharaɗin mayakan Hamas za su saki dukkan ‘yan Isra’ilan da suke garkuwa da su.

Wannan na zuwa ne yayin da Isra’ila ke ci gaba kai hare-hare a sassan Zirin Gaza, ciki har da Rafah, birnin da dakarun Isra’ila ke shirin aukawa da yaƙi ta ƙasa.

Kasashen Masar, da Amurka, da Qatar ne ke ta kokarin shiga tsakani a tattaunawar neman kulla yarjejeniyar tsagaita wutar.

Sai dai har zuwa wannan lokaci Hamas ba ta ce komai kan tayin da aka gabatar ma ta ba, ko da ya ke dama ta sha nanata cewa, ba za ta amince da wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ba, har sai Isra’ila ta janye dakarunta bakiɗaya daga Zirin Gaza, ta kuma dakatar da kai hare-hare ta sama, domin ba Falasɗinawa damar komawa tsirarun gidajen da suka rage da ba a ragargaza ba.

A baya-bayan nan kuma, sakataren harkokin wajen na Birtaniya, ya ce muddin ana son cimma burin samar da kasar Falasɗinu, to wajibi ne duk wani mai hannu a harin da aka kai wa Isra’ila a watan Oktobar bara ya fice daga Zirin Gaza, kuma tilas sai an rushe duk wani abu da mayakan Hamas suka mallaka a yankin.

RFI              AAG

Latest stories

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data kirkiri masarautun...

Related stories

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data kirkiri masarautun...