Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNan da mako biyu za a fara jigilar maniyyatan jihar Kebbi.

Nan da mako biyu za a fara jigilar maniyyatan jihar Kebbi.

Date:

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, Alhaji Faruk Musa-Enabo, ya ce nan da mako biyu za a fara jigilar maniyyatan jihar zuwa kasa mai tsarki domin aikin hajjin bana.

Tuni da ma hukumar aikin hajji ta kasa, da hukumar kula da filayen jiragen sama suka yi alkawarin bayar da damar fara amfani da tashar jiragen sama ta Sir Ahmadu Bello International Airport, da ke Birnin Kebbi, domin jigilar alhazan bana.

Rahotanni kuma sun tabbatar da cewa, an samar da dukkan kayayyakin aikin da suka kamata a filin jirgin saman, saboda haka a shirye ya ke a fara amfani da shi ranar 15 ga wannan wata na Mayu, domin daukar maniyyata zuwa Saudiyya.

Shugaban hukumar jin dadin alhazan na Kebbi, ya shaidawa kwamitin aikin hajjin na bana cewa, jirgin farko da zai tashi, zai dauki maniyyata 423, da suka fito daga yankunan kananan hukumomin Jega, da Arewa, ciki har da jami’an da zasu lura da alhazai, yayin da jirgi na biyu kuma, shi zai dauki maniyyata 423, na yankunan kananan hukumomin Argungu, da Dandi.

Maniyyatan kananan hukumomin Kalgo, da Aliero, da Bunza, da Gwandu, su ne za su kasance a jirgi na uku, in ji Alhaji Farouk Musa-Enabo.

 

NAN                        AAG

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...