Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn haifi Muhammad Mokhbar a shekarar 26 ga watan Uni na 1955...

An haifi Muhammad Mokhbar a shekarar 26 ga watan Uni na 1955 a Khuzestan.

Date:

An haifi Muhammad Mokhbar a shekarar 26 ga watan Uni na 1955 a Khuzestan.

Yanzu haka yana da shekaru 68 a duniya.

Ya yi digirinsa ta farko a fannin injiniyan latroni, da digiri na biyu a fannin gudanarwa da tsare-tsare, sannan kuma ya yi digirinsa na uku a fannin shari’ar duniya.

Tsohon jami’in kare juyin juya hali ne a lokacin yaƙin Iran da Iraki a shekarun 1980 zuwa 1988.

A baya ya kula da sashen kiwon lafiya a yankinsu, ya kuma yi mataimakin gwamnan Khuzestan, da shugaban wani banki mai zaman kansa.

Sannan ya koma gudanar da cibiyoyin kasuwanci da ke kusa da ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ali Khamenei.

Muhammad Mokhbar yana da mata da ƴaƴa 2.

Latest stories

Related stories