Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta...

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

Date:

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nemi ɗaukin gaggawa domin kawar da matsalar tsaro da ta yi silar ƙarancin abinci a jihar, da ma yankin Arewa maso yammacin kasar nan.

Ya bayyana haka ne a wani taro kwanan nan a Abuja, tsakanin jami’an gwamnatin Katsina da wakilan hukumar samar da abinci ta duniya.

Babban sakataren labaran gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Muhammad, da ya sanar da haka, ya jaddada ƙudirin gwamnatin na tallafawa al’ummar jihar.

Sanarwar ta kuma ruwaito Gwamna Radda na godewa wakilan hukumar samar da abinci ta duniya ƙarƙashin jagorancin daraktan ƙasa, David Stevenson, saboda amincewa da yankin Arewa maso Yamma a matsayin ki mai mahimmanci da ke buƙatar taimako.

Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa tun da ta hau ofishin kusan shekara guda da ta wuce ya fara yunƙuri don yaƙi da rashin tsaro, amma halin da ake ciki yanzu akwai tarin ƙalubale a lamarin.

Latest stories

Related stories